Skip to main content

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Shiga Tsaka Mai Wuya - Bello Muhammad Sharada

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Shiga Tsaka Mai Wuya - Bello Muhammad Sharada

Shin Muhammadu Buhari Zai Sami Kuri’a Miliyan Biyar a Kano, Miliyan Uku a Jihar Legas Kuwa?

A wurare da yawa na taron siyasa, gwaman jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje yana cewa idan an zo zaben shekarar 2019 na shugaban kasa, jihar Kano za ta baiwa shugaban kasa kuri'a miliyan biyar.

Gwamna Ganduje ya fara fadar haka ne bayan an yi zaben kananan hukumomi a Kano, kusan shekara guda da ta gabata. A wannan zaben da ciyamomi 44 a Kano da kansilolinsu 484 duka jam'iyyar APC ce ta cinye su. Kansila daya ba jam'iyyar da ta samu.

A kwanan nan kuma jaridu da yawa sun rawaito Bola Ahmed Tinubu, jagoran APC a Lagos da Najeriya yana maimaita wa a wuraren tarukan siyasa cewa daga jihar Lagos kuri'ar da shugaban kasa PMB zai samu a wannan zaben miliyan uku ce.

A gwarance da jihar Kano da jihar Lagos, jiha biyu cikin 36 kacal, sun sha alwashin kawo wa PMB kuri'a miliyan takwas, wato sama da kashi 50 na yawan kuri'ar da Buhari ya samu a zaben shekarar 2015.
Nufina a wannan tsokacin na amsa tambayoyi guda biyu. 

Ta farko shin shugaban kasa zai iya samun kuri'a miliyan biyar a jihar Kano, kamar yadda gwamna Ganduje ya daukar masa alkawari? Shin a jihar Lagos za a iya baiwa Buhari kuri'a miliyan uku a ranar zabe?
Watakila idan muka samo wannan amsar zai taimakawa wadanda suke lura da shirya dabaru da tsarin cin zabe, su sake kallon al'amarin. Inda za a gyara a gyara, inda za a inganta a inganta shi. A wani gurin kuma a sake lale.

Wannan tsokacin ya yi la'akari da alkaluman zabukan da aka yi a Kano da Lagos daga shekarar da Buhari ya fara shiga zabe ta 2003 zuwa lokacin da ya yi nasara a 2015.
A shekarar 2003 da Buhari ya bayyana a dan siyasa, kuma dan takarar jam'iyyar ANPP na shugaban kasa, an yi zabe a Kano da Lagos. Sakamakon zaben shi ne, Buhari ya samu kuri'a 1,628,085 a Kano. A Lagos kuma 116, 510. A wannan shekarar mutanen Kano da suka yanki katin zabe jumlarsu 4,000,814.

Yanayin da aka shiga wannan zaben shi ne, Buhari sabo ne kuma mai ceto. Ana cikin shaukin guguwar da ta taso ta shari'ar Musulunci. Musulmi suna ganin Buhari a wani nasiruddin. Akwai kabilanci kudu da arewa. 

A lokacin Obasanjo ya yi wa mutanen arewa laifi suna son ramawa kuma ga shi Kirista. Haka kuma manyan dakaru masu kishin Najeriya da arewa sun yi guruf mai karfi da sunan THE Buhari Organisation TBO. Buharin kawai suke kallo. Ita kuma Jam'iyyar ANPP ta Buhari tana da gwamnoni da masu fada a ji, kuma a dinke guri guda. Da PDP da dan takararta na shugaban kasa suna da bakin jini sosai a gun mutanen arewa. Da aka yi zaben sai Kanawa suka yi fitar dango suka zabi Buhari. Kuri'ar da OBJ ya samu ita ce 492, 755 a lokacin PDP ce take da gwamna da sanatoci da 'yan majalisar tarayya da na jiha da ciyamomi da kansiloli. Asalin SAK ta farko kenan.

A shekarar 2007 ANPP ta sake tsayar da Buhari. Ya samu kuri'a 1, 069, 127 a Kano. A Lagos kuma ya samu 66,411. Kuri'ar Buhari baya tayi sosai a Kano da Lagos. A wannan shekara mutanen da suka yanki katin zabe daga Kano yawansu 4,072,597. A Lagos kuma yawansu ya kai miliyan hudu.

Ita shekarar 2007 ta zo wa Muhammadu Buhari da sauyi. Abokin takararsa Ummaru Musa 'Yar Aduwa ba kawai dan arewa Musulmi bane, a'a dan jihar Katsina ne mahaifar Buhari, kuma gwamna mai ci. Da gwamnonin Arewa na ANPP da dattawan arewa kansu ya rabu. 'yan TBO suna nan daram amma suna rigima da jam'iyya da wasu gwamnoni har da na Kano. 

Sannan kuma Obasanjo a matsayinsa na shugaban kasa ya kudure a zuciyarsa koda 'tsiya ko da tsiya-tsiya' sai PDP ta koma. Amma kuma a wannan shekarar ANPP ce ke mulkin Kano.
Ganin halin da ya shiga a 2003 da 2007, 'yan TBO da masu labewa da Buhari don samun takara suka ga wuyansu ya yi kauri kuma sun yi tsammanin ba zasu samu gagarumin goyon baya ba daga gwanonin ANPP, sai suka kafa sabuwar jam'iyya ta CPC. 

A shekarar 2011 da aka yi zabe a Kano Buhari ya samu kuri'a 1,624,354. A Lagos kuma ya samu 189, 983 duka a CPC. A Kano a wannan shekara PDP ta samu kuri'a 440,666, a Lagos kuma ta samu 427,000.

Shekarar 2011 ita ce Buhari ya yi kuka da hawaye kuma ya yi alkawarin ba zai sake neman takara ba, kuma da zai ci zabe, zango daya kawai zai yi. Zaben 2011 shi ne mafi muni da tashin hankali. An samu tsananin tsoro da gaba a tsakanin arewa da kudu da Musulmi da Kirista, sakamakon rasuwar Yar Aduwa da matsayin da dattawan arewa karkashin Adamu Ciroma suka dauka na yakar Jonathan da wanda su kuma dattijan kudu tare da goyon bayan Obasanjo suka dauka na goyon bayan Jonathan.

An kashe dan adam, an kona dukiya bayan fitar da sakamakon zaben 2011. Tun daga 2003, har zuwa 2015 shekaru 15 cur babu lokacin da babu matsalar tsaro ko ta kabilanci ko addini ko Neja Delta ko ta tattalin arziki a sassan kasa.

A shekarar 2015 fasalin siyasar Buhari ya sauya. Aka tabbatar da dangantaka da aka fara kullawa a 2011 da yankin Yarbawa. Shekarar ta zo da yanayi mai kyau ga Buhari. Ya hada kai da Yarbawa. Ya samu goyon bayan manyan kasashen duniya. Da dattijai na kasa da 'yan siyasa masu rike da gwamnati sun karbe shi. Ya samu jam'iyyar hamayya mai karfi. Jama'ar kasa sun gaji da mulkin PDP. 

A arewa an sanya kafar wando daya da Jonathan. Kasuwar sabuwar kafar sadarwa ta social media tana ci sosai kuma tana yi da Buhari. Ga kudi ta ko ina zuwa suke masa.
Da aka yi zaben 2015 a Kano Buhari ya samu kuri'a 1,903, 999, a Lagos kuma ya samu 792,460. A shekarar PDP a Kano abin da ta samu 215, 799, a Lagos kuma PDP ta samu 632,327.

Tunda Buhari ya fara zabe a Kano yana samu kuri'a sama da miliyan daya. Bai taba samun kuri'a dubu 200 ba a Lagos sai a 2015. Goyon bayan Buhari ya fi samuwa idan sun hada takara da dan kudu wanda ba Musulmi ba. A shekara daya ne tal PDP ba ta samu kashi 25 na yawan kuri'ar da take nema don biyar bukatarta ta zabe ba, ita ce 2015.

Tambaya, daga wannan lissafin zai yiwu Buhari ya samu kuri'a miliyan biyar a Kano bisa alkawarin Ganduje ko miliyan uku a alkawarin Bola Tinubu? Sam-sam ba zai yiwu ba, kuma in an riga an hada lissafi don Allah a gyara.

Dalilan da zasu sa ba za a sami wannan kuri'a ba sune. A bana masu katin zabe a Kano su 5,459,914, a jihar Lagos kuma 6, 570,291. A yanayin fita zabe tun daga shekarar 1999 kashi 50 ne suke fita, saura zamansu a gida suke yi. Magana ta gaskiya da yawan mutanen Kano basu ganin armashin wannan zaben kamar na 2015, za a samu karancin fita sosai, saboda duk zaton da suka yi wanda ya sa suka yi zaben Buhari tun 2003, sun ga bambanci da basu sa rai ba. A Lagos su Tinubu sun samu biyan bukatarsu, amma a cikin gida akwai matsala,sannan sam mutanen Lagos ba sa fitowa zabe.

Abu na biyu a Kano dakarun Buhari sun tarwatse. Ba Buba Galadima, ba Najaatu. Ba Jaafru Isa. Ba Dan Zago. Su Sule Halilu da Isa Bayero da Sule Hamma sun yi gum da bakinsu. Dadi da kari, yanzu da akwai sabani a tsakanin mutanen Ganduje da Kwankwaso da Shekarau da Buhari, babu ittifakin haduwa don yin aiki akan nasararsa. Kowa kansa kawai.

Abu na uku, za a yi takara ne tsakanin musumli da musumli, Bafulatani da Bafaulatani, dan arewa da dan arewa, APC mai gwamnati da PDP mai rangwamen bakin jini. Ba za a yi taron dangi irin na shekarar 2003 ko 2015.

A Lagos wadanda suka yi Buhari a baya suna na daram, suma kuma wanda suka yake shi suna nan daram.
A fahimtata sai Buhari ya yi da gasken gaske, sannan su Dr. Baffa Bichi da DanBalki Kwamanda za su tattaro masa kan kuri'a miliyan biyu a Kano, su Tinubu su tattara masa miliyan daya a Lagos. Zai yi kyau jama'ar Buhari su sake kallon Kano da Lagos a tsanaki, kada su kuskura su dogara da lissafin duna. Ba a taba yi ba, kuma ba za a fara ba. Sai dai in za a maimaita salon Obasanjo na 2007.

Comments

Popular posts from this blog

https://www.fitila24.com.ng/2019/01/wasu-yan-bangar-siyasa-sun-kai-hari.html?fbclid=IwAR23mCRaVT0MpvEh440-WZA67F655sytOCchC4318fPKoa-cTWWeeWkB6TA

Asirin APC Ya Tonu! Alkawarin da Buhari Ya yiwa Shugaban INEC Idan Ya Mika masa Mulkin Najeriya 2019.

Internet and Computer Abbreviations and their full meanings‎