Skip to main content

Asirin APC Ya Tonu! Alkawarin da Buhari Ya yiwa Shugaban INEC Idan Ya Mika masa Mulkin Najeriya 2019.

Asirin APC Ya Tonu! Alkawarin da Buhari Ya yiwa Shugaban INEC Idan Ya Mika masa Mulkin Najeriya 2019.



Tsohon sakataren yada labarai na kasa a jam’iyyar APC Kwamared Timi Frank, ya bayyana cewa jam’iyya mai mulki ba ta neman ‘yan Najeriya su sake zaben ta saboda ta san za ta fadi zabubbukan ta masu zuwa.

Timi ya kara sa cewa “Mun san shugaban hukumar zabe na kasa yayi wata ganawar sirri da shugaban kasa Buhari a fadar sa dake Abuja, kuma muna so ya sani idan ya bawa Buhari zaben 2019 to babu shakka Najeriya zata iya kamawa da wuta”

Tsohon mai maigana da yawun jam’iyyar APC ya nuna tabbacin sa akan batun cewa tarihi zai maimaita kan sa, yadda aka kada gwamnati maici a jamhoriyar dimokuradiyyar Congo haka zaben shugaban kasar Najeriya mai zuwa za’a kada Buhari.

Frank yace kasashen Afirika sun nuna matukar gajiyar su da shugabannin mulkin kama karya, kuma kada gwamnatin Joseph Kabila da a kayi a zaben da ya gudana kwanan ya nuna cewa tabbas ‘yan Afirika sun gaji da shugabanni masu mulkin kama karya.

“Muna amfani da wannan dama don jan kunnen shugaban hukumar zabe na kasa da duk wadanda suke ganin zasu yi wani abu da ya  sabawa abinda ‘yan Najeriya suke so to su aje wannan yunkuri nasu, domin mafiya yawan ‘yan Najeriya ba zasu sake zaben gwamnatin da wasu mutum biyu ne suke juya ta ba a zaben 2019.” A cewar Frank.

Da yake jan kunnen shugaban hukumar zabe ta INEC yace kada shugaban ya bari Najeriya ta kama da wuta, cikin abinda ya bayyana shi a matsayin mummunar manufa ta murdiyar zabe, Frank ya bukaci a rarrabe wajen tantance masu zabe da wajen da ake zabe.

Timi Frank yace “Muna da masaniyar an yi wata ganawar sirri a fadar shugaban kasa an kuma yiwa shugaban hukumar zabe ta kasa alkawarin idan ya rubuta Buhari yaci zaben 2019 za’a bashi rijiyar mai a Najeriya”

Comments

Popular posts from this blog

https://www.fitila24.com.ng/2019/01/wasu-yan-bangar-siyasa-sun-kai-hari.html?fbclid=IwAR23mCRaVT0MpvEh440-WZA67F655sytOCchC4318fPKoa-cTWWeeWkB6TA

Internet and Computer Abbreviations and their full meanings‎