Skip to main content

https://www.fitila24.com.ng/2019/01/wasu-yan-bangar-siyasa-sun-kai-hari.html?fbclid=IwAR23mCRaVT0MpvEh440-WZA67F655sytOCchC4318fPKoa-cTWWeeWkB6TA


‘Yan bangar siyasa a jihar Kwara wanda ake zargin ‘yan jam’iyyar APC ne, sun kai hari gidan shugaban majalisar dattawar Najeriya Dr. Bukola Saraki.

An bayyana cewa ‘yan bangar siyasar sun bude wuta kan mai uwa da wabi ne a gidajen al’ummar dake unguwar Agbaji, inda suka raunata mutane 11.

‘Yan jagaliyar Sun lalata motoci 50 dake ajiye a cikin gidan Sarakin dake Kwatas din Agbaji.

A cewar shugaban Agbaji Development Association, Alhaji Musa Olanrewaju Yusuf ‘yan jagaliyar siyasar sun aikata wannan ta’addanci ne a karkashin shugaban su Yahaya Seriki da kuma Musbahu Esinrogunjo.


Musa, wanda kuma shine shugaban Agbaji Development Association yace mutane 11 ne suka sami munanan raunuka sakamakon harbin su da aka yi da bindiga a yayin wannan hari da ‘yan ta’addan suka kai an kuma dauke su zuwa babban asibitin jihar Ilorin da asibitocin kudi don nema masu lafiya. 

Comments

Popular posts from this blog

Asirin APC Ya Tonu! Alkawarin da Buhari Ya yiwa Shugaban INEC Idan Ya Mika masa Mulkin Najeriya 2019.

Internet and Computer Abbreviations and their full meanings‎